'Shekau ya fadi inda yake a Sambisa in gaskiya ne'

Asalin hoton, AFP
Rundunar sojin ta ce Boko Haram na son kawai ta sanya tsoro ne a zukatan mutane
Rundunar sojin Nigeria ta kalubalanci shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau da ya fadi in da yake a dajin Sambisa in da gaske ne ikrarin da ya yi cewa sojojinta ba su fattake su daga can ba.
A ranar Alhamis ne dai wani faifan bidiyo ya bulla dake nuna Shekau din yana musanta kalaman da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a makon jiya cewa dakarun kasar sun fatattaki mayakan Boko Haram daga dajin na Sambisa.
Sai dai rundunar ta bayyana bidiyon da cewa farfaganda ce kawai kuma za ta yi nazari a kansa.
''Ba wani wuri da suke yanzu a dajin Sambisa, kuma in ya ce suna nan, ya gaya mana a ina ne yake a Sambisa ai yaranmu na wurin.'' In ji Birgediya-Janar Rabe Abubakar kakakin hedikwatar tsaron kasar cikin wata hira da BBC.
A faifan bidiyon mai tsawon mintuna 25 dai, Shekau ya yi ikrarin cewa "Muna nan da ranmu da lafiyarmu. Babu wanda ya kore mu daga wani wuri."