Cin hanci: Natanyahu zai fuskanci binciken 'yansanda

Benjamin Natanyahu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana tuhumar ya karbi kyautar kudi masu yawa daga wasu 'yan kasuwa.

Rahotanni daga kasar Isra'ila sun ce rundunar 'yansandan kasar ta bukaci jami'an ofishin Farayin Minista Benjamin Natanyahu da su ware ma sa lokacin da zai je domin amsa tambayoyi kan tuhumar yin almundahana.

Matakin ya zo ne kwana daya bayan da Atoni-janar na kasar Avichai Mandelblit ya amince da a yi wa farayin ministan binciken kwa-kwaf.

Tashar gidan Tallabiji ta Channel 10 da ke kasar ta Isra'ila ta ce yanzu haka ofishin farayin ministan na can na kokarin samun lokacin da ya yi wa Natanyahu daidai da ya je ya amsa tambayoyin.

Kafar watsa labaran ta ce manyan tuhumce-tuhumcen da ake yi wa Mr. Natanyahu su ne zamba-cikin-aminci da kuma karbar kyaututuka ba bisa ka'ida ba.