'Dansandan Brazil ne ya kashe jakadan Girka'

Kyriakos Amiridis

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

An dai kona gawar Mr. Amiridis bayan kashe shi.

'Yansanda a Brazil sun ce wani dan sandan kasar da ke kwartanci da matar jakadan Girka a kasar ne ya kashe shi.

A ranar Litinin ne dai jakadan Kyriakos Amiridis ya bace, inda daga bisani aka gano gawarsa cikin wata konanniyar mota a wajen birnin Rio-de-Janeiro ranar Alhamis.

'Yansandan suka ce dansandan, Sergio Gomes Filho, ne da kansa ya yi ikrarin cewar shi ne ya shake jakadan har ya mutu.

A halin yanzu dai ana tsare da matar jakadan - wadda 'yar kasar Brazil ce - Francoise Amiridis da Mr. Filho da kuma dan baffansa.

Jakadan mai shekaru 59 dai na kan hanyarsa ne ta zuwa birnin Nova Iguacu, arewa ga birnin Rio domin yin hutu kirsimati a can tare da matar tasa da kuma iyayenta lokacin da aka kai masa hari.