Buhari ya yi kira ga 'yan Shi'a su zauna lafiya

Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Buhari ya ce 'yan Najeriya za su dara

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci 'ya'yan kungiyar 'yan uwa Musulmi wadanda aka fi sani da 'yan Shi'a da su rungumi turbar zaman lafiya.

Shugaban ya bayyana haka ne a sakonsa na sabuwar shekara.

Shugaba Buhari ya ce, "A matsayinsu na 'yan uwanmu, muna kira ga 'yan Shi'a su rungumi turbar zaman lafiya. Dole su bi dokokin kasar da suke zaune a ciki".

Ya kara da cewa, "A lokaci guda kuma, dole jami'an tsaro su rika mu'amala da su ta hanyoyin da suka dace da kuma bin doka kan yadda suke tunkararsu".

Hakan na zuwa ne dai a yayin da 'yan Shi'a ke ci gaba da korafi kan zargin gallazawar da jami'an tsaron kasar ke yi musu.

Hukumomin kare hakkin dan adam irin su Amnesty International sun ce jami'an tsaron na Najeriya sun kashe daruruwan 'yan Shi'a a lokacin da suka bude musu wuta a birnin Zaria a watan Disambar shekarar 2015.

Bayan haka ne suka kama shugaban kungiyar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa da wasu manya-manyan 'yan kungiyar inda har yanzu suke ci gaba da tsare su duk da hukuncin da kotu ta yanke na sakin su.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan Avengers sun kassara tattalin arzikin Najeriya

'Zaman lafiya a Naija Delta'

Shugaba Buhari ya kuma ce zai ci gaba da neman zaman lafiya da mazauna yankin Naija Delta mai arzikin man fetur.

A cewarsa, "ina jaddada kira ga 'yan uwana na yankin Naija Delta wadanda suke tayar da kayar-baya da kuma yin zagon-kasa ga tattalin arzikin kasa da su zo mu sasanta."

Sai dai shugaban na Najeriya ya ce za su tunkari duk wani mutum da ba ya kaunar zaman lafiya, yana mai shan alwashin cewa ba zai bar wani ko wata su durkusar da Najeriya ba.