Wani soja ya harbe kwamandansu a Somaliya

somalia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jami'an tsaro a Somaliya

Rahotanni daga Mogadishu babban birnin Somaliya sun ce wani soja dake cikin jami'an tsaro dake gadin fadar shugaban kasar ya harbe kwamandansu har lahira.

Rahotannin sun ce an harbe Kanar Abdi Abdulle Qoorgaab ne a cikin fadar shugaban kasar.

An kuma jin karar harbe-harbe daga cikin fadar, sannan wani soja kuma ya jikkata.

Ba a dai san dalilin da ya sa sojan kashe kwamandan na su ba.

A Bangladesh kuma, wasu 'yan bindiga sun harbe wani dan majalisar dokokin kasar a gundunar Gaibandha dake arewacin kasar.

'Yan sanda sun ce wasu mutane uku ne suka harbe Manjurul Islam na jam'iyyar Awami League mai mulki a kasar lokacin da suka shiga gidanshi shi.

Ba a gano ko su wanene suka kashe dan majalisar ba.