An daure wasu likitoci a China kan dashen koda

Kidney transplant

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Aikin dashen koda a wani asibiti

An yankewa wasu mutane goma sha shida, akasarinsu kwararrun jami'an lafiya, hukuncin daurin shekaru biyar a kurkuku a China, saboda sun yi tiyatar dashen koda ba bisa ka'ida ba.

Mutanen wadanda suka fito daga lardin Shandong, sun hada da likitoci biyu, da mai kashe radadin tiyata, da kuma ungozoma.

Mutanen sun samo wadanda ke so su sayar da kodar su, da kuma masu bukatar a yi musu dashen ta ne.

Sun caji masu so a yi musu dashen kodar kusan dala dubu sittin akan koda daya, amma kuma, suka biya mutanen da suka bayar da kodar ta su dala dubu shida kowacce daya.

Karancin masu sha'awar taimakawa da kodar a China dai, ya sa kasuwa ta budewa masu dashen kodar.