An tsaurara matakai yayin da shekarar 2017 ke kamawa

Asalin hoton, AP
Tuni Singapore da wasu kasashen Asia suka shiga sabuwar shekarar
An tsaurara matakan tsaro a manyan biranen duniya yayin da ake shirin shiga sabuwar shekara ta 2017.
A wasu biranen kasashen yamma, da suka hada da London, da Brussels da Berlin, an girke karin dubban 'yan sanda gabanin bukukuwan shiga sabuwar shekarar.
An sanya shingaye na kankare a wuraren taruwar jama'a a tsakiyar birnin Paris, da Madrid da New York don kare aukuwar hare-hare da manyan motoci, kwatan-kwacin wadanda aka kai a baya a biranen Berlin da Nice.
An hana jama'a yin shagulgulan sabuwar shekarar a Dhaka, babban birnin Bangladesh, wanda ya yi fama da hare-haren 'yan bindiga masu alakanta kansu da Musulunci.
Asalin hoton, Reuters
Masu murnar shiga sabuwar shekara a birnin Beijing na China