Wani dan bindiga ya kashe mutum 39 a Turkiyya

Wasu daga cikin wadanda suka ji rauni ke nan
Wani mutum dauke da bindiga ya kashe mutum 39 sannan ya jikkata 40, a wani hari da ya kai gidan rawa.
Harin wanda aka kai a birnin Istanbul na Turkiyyar, ya janyo mutane da dama sun kuma fada cikin kogi sakamakon gudun ceto rai.
Kididdiga dai ta nuna akwai mutum fiye da 700 a gidan rawar lokacin da abin ya faku.
Kafofin watsa labaran kasar sun ce mutumin ya yi shigar burtu ne, har ya samu ya shiga gidan rawar.
Daga nan kuma sai ya bude wuta a inda nan take ya kashe mutanen.
Rahotannin dai sun tabbatar da cewa dan sanda daya na daga cikin mamatan.
Daman dai akwai 'yan sandan ko-ta-kwana fiye da dubu 16 a birnin na Istanbul saboda yawaitar hare-haren ta'addanci.
Ko a makonni biyun da suka gabata ma sai da aka harbe jakadan kasar Russia har lahira.
Sau shida ne dai hare-haren da ke haddasa mutuwa da jikkatar mutane suka faru a 2016 a kasar musamman a biranen Ankara da Istanbul.
Kuma fiye da mutane 200 sun mutu a hare-haren guda shida.
Asalin hoton, AP
Motocin daukar marasa lafiya na zurga-zurga