Ni ma zan iya amfani da karfi kan ECOWAS — Jammeh

Jammeh

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yahya Jammeh ya jagoranci Gambia shekara 22

Shugaban Gambia mai barin gado, Yahaya Jammeh, ya ce, idan tura ta kai bango zai iya yakar Kungiyar Habaka Tattalin arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS ko kuma CEDEAO.

A wani sakon taya murnar sabuwar shekara ga 'yan kasar, da aka yada a kafar sada zumunta ta Youtube, Jammeh, ya ce, kungiyar na wuce gona da iri a Gambia.

Ya ce ECOWAS na nuna banbanci tsakaninsa da Adama Barrow.

Saboda haka ne ya nemi kungiyar da ta san inda dare ya yi mata domin a cewarsa bata da hurumin yin katsalanda a kasar.

Yahya Jammeh dai ya ce shi ne mutumin da ya lashe zaben kasar na farkon watan Disambar 2016, bayan da da fari ya amince da shan kaye.

Kungiyar ECOWAS dai a taron da ta yi a Abuja, babban birnin Najeriya, ta ce, za ta iya amfani da karfi wajen tunbuke Yahya Jammeh.