Wani mutun ya halaka tsohuwar matarshi a Brazil

Brazil

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wata unguwa a kasar Brazil

'Yan sanda a Brazil sun ce mutane da dama ne aka kashe, lokacin da wani mutun dauke da muggan makamai ya kutsa cikin wani gida inda tsohuwar matar shi ke yin shagalin shiga sabuwar shekara.

Mutumin ya harbe tsohuwar matar ta shi, da yaron su mai shekaru takwas, da kuma sauran 'yan uwanta da dama.

Daga nan kuma, mutumin ya harbe kan shi shima.

Wasu mutane uku sun jikkata a lamarin, wanda ya auku a birnin Campinas dake kudu maso gabashin kasar.