''Yan Shi'a su zargi hukumomin tsaro ba Buhari ba'

'Yan Shi'a

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rahotanni sun ce an ji wa El-Zakzaky munanan raunuka

Mai taimaka wa shugaban Najeriya na musamman kan harkar yada labarai, Malam Garba Shehu, ya ce, bai kamata 'yan Shi'a su zargi Buhari ba kan kin sakin shugabansu, Sheikh El-zakzaky ba.

Ya ce duk da cewa kotu ta yanke cewa a saki Sheikh Zakzaky amma kuma akwai wasu da suka shigar da daukaka kara kan batun.

Ya kuma kara da cewa baya da batun daukaka kara akwai kuma wasu rahotannin tsaro da hukumomin tsaron kasar su ma suke dogara da su.

Malam Garaba Shehu ya ce, ya kamata 'yan Shi'ar sun sani cewa Buhari ba shi da hannu a shari'ar da ake yi wa shugaban nasu.

Sannan kuma ba shi da hannu kan kwamitin bincike da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa wanda ya ba da shawarar haramta kungiyar.

Daga karshe malam Garba ya shawarci mabiya mazhabin na Shi'a su jira abin da shari'a za ta yanke nan gaba.

Kungiyar 'yan uwa Musulmi wadda aka fi sani da Shi'a dai ta bukaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya saki shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky kamar yadda kotu ta ba shi umarni maimakon kiran da ya yi musu na su zauna lafiya.

A jawabinsa na sabuwar shekara Shugaba Buhari ya ce, "A matsayinsu na 'yan uwanmu, muna kira ga 'yan Shi'a su rungumi turbar zaman lafiya. Dole su bi dokokin kasar da suke zaune a ciki".

Ya kara da cewa, "A lokaci guda kuma, dole jami'an tsaro su rika mu'amala da su ta hanyoyin da suka dace da kuma bin doka kan yadda suke tunkararsu".

Sai dai a wata sanarwa da kakakin kungiyar Ibrahim Musa ya aike wa manema labarai, ya ce Shugaba Buhari shi ne mutumin da ba ya bin dokokin Najeriya domin kuwa sau da dama kotu na bayar da umarnin a saki Sheikh El-Zakzaky amma har yanzu gwamnatin kasar ta ki yin biyayya ga hukuncin kotun.

'Ba ya yin biyayya ga kotu'

Ya kara da cewa, "Shugaban kasa, har yanzu ba ka bi umarnin kotu ba na sakar shugabanmu, Sheikh Ibraheem Zakzaky, wanda aka tsare ba bisa ka'ida ba kuma ba tare da an tuhume shi ba, fiye da shekara daya duk da umarnin da kotu ta bayar na yin hakan."

Sanarwar ta ce, "Ko a makon jiya lauyanmu Femi Falana (SAN) ya rubuta maka [Buhari] wasika inda ya yi maka tuni a kan hakan ta hannun ministan shari'a. Don haka ya kamata ka yi biyayya ga dokokin kasa ta hanyar bin umarnin kotu ka saki Sheikh Zakzaky ba tare da bata lokaci ba".

Ibrahim Musa ya ce matakin da suka dauka na zuwa kotu duk da cin zarafin da dakarun tsaron Najeriya suka yi mus ya nuna cewa kungiyarsu tana matukar kaunar zaman lafiya sabanin kashin-kajin da ake shafa mata cewa ita mai son tayar da zaune tsaye ne.

Sanarwar ta yi kira ga Shugaba Buhari ya saki dukkan 'ya'yan kungiyar da ake tsare da su tun bayan dirar-mikiyar da aka yi musu a birnin Zaria a watan Disambar shekarar 2015, kana a hukunta jami'an tsaron da suka kashe 'yan kungiyar a Zaria, Kaduna, Kano, Funtua da kuma Sokoto.

Hukumomin kare hakkin dan adam irin su Amnesty International sun ce jami'an tsaron na Najeriya sun kashe daruruwan 'yan Shi'a a lokacin da suka bude musu wuta a birnin na Zaria bayan sun zarge su da yunkurin kashe shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, zargin da suka sha musantawa.