Myanmar ta amince da azabtar da musulmi

Bangladesh

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan sanda sun ce mutane dubu 6 ne suka shirya wa zanga-zangar

A karon farko, hukumomi a Myanmar sun amince da cewa 'yan sandar jihar Rakhine suna azabtar da musulmai 'yan kabilar Rohingya.

Yanzu gwamnatin kasar dai ta alwashin daukar matakin hana afkuwar hakan a gaba.

Wannan dai ya biyo bayan bazuwar a kafafen sada zumunta, wanda ya nuna yadda jami'an tsaron suke dukan azabtar da 'yan kabilar ta Rohingya.

Bidiyon ya nuna wasu 'yan kabilar ta Rohingya da dama da aka kama, a zaune, a dandaryar kasa kuma hannuwansu bisa kawunansu.

Sannan an ga wani dan sanda yana tafkar wani daga cikin mutanen da sanda, kafin kuma wani dan sandan shi ma ya sa kafa yana tattaka shi.

'Yan sandan ne dai suka dauki hotunan da kansu.

A baya dai an sha bayyana irin wadannan bidiyo da 'yan kabilar ta Rohinja ke dauka da kansu da na jabu.