Niger: Jam'iyar MPN Kiishin Kassa ta kori mutum 13

Taron MPN
Bayanan hoto,

'Yan jam'iyar MPN a Nijar

Jam'iyar MPN Kishin Kasa, ta yi bikin cika shekara daya da kafuwa.

Sai dai kuma a daidai lokacin ne kuma ta kori wasu 'ya 'yan ta 13.

Daga cikin wadanda MPN ta kora, har da mataimakin shugaban jam'iyar na kasa, Sani Atiya daga jihar Maradin Katsina.

Kwomitin koli na jam'iyar ya kori mutanen ne guda 13 saboda abun da ya kira sabawa dokokin jam'iyar da su ka yi.

An dai shafe watanni da dama ana kokarin dinke barakar da ta kunno kai a cikin jaririyar jam'iyar amma lamarin ya ci tura.

'Ya 'yan jam'iyar da aka kora na ikirarin cewa ana son mayar da jam'iyar ne tamkar wata kabila.

To sai dai kuma shugaban jam'iyar, Ibrahim Yacouba ya jaddada cewa wannan kora da aka yi wa mutanan guda 13 shi ne abu mafi alheri ga jam'iyar.

Ya kara da cewa jam'iyar ta matasa ce, sannan ana yi komai bisa nutsuwa da tsari.