Ana farautar dan bindiga a Turkiyya

'Yan sanda na neman dan bindiga
Jami'an tsaro na ci gaba da farautar dan bindigar nan ya kashe mutum 39 a wani gidn rawa a birnin Santanbul na Turkiyya.
Tuni dai aka riga aka yi zana'izar mutanen da suka mutu.
Rahotanni sun sanar da cewa da dama daga cikin wadanda suka mamatan 'yan kasashen larabawa ne.
Kuma biyar daga cikinsu sun fito daga Saudiyya.
Tuni dai shugaban kungiyar Kurdawa ta PKK masu gwagwarmaya da makamai a kasar ta Turkiyya, ya musanta kungiyar na da hannu a harin.
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da harin.
Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya ce ya na da tsananin wuya a yi tunanin aikata kai irin wannan mumunan hari.
Shi ma Paparoma Francis, ya nemi al'ummar duniya baki daya da su dauki matakan dakusar da ta'adanci.