Kungiyar IS ta dauki alhakin kashe mutum 39 a Turkiyya

Bayanan bidiyo,

Bidiyo: Yadda maharin Turkiyya ya isa gidan rawar da ya kashe mutum 39

Kungiyar IS da ke ikirarin kafa daular Musulunci ta dauki alhakin harin da ya kashe mutum 39 a wani gidan rawa a Turkiyya.

Akalla masu shakatawa 600 ne suke bikin sabuwar shekara a gidan rawa na Rena a lokacin da dan bindigar ya fara harbi kan mai-uwa-da wabi.

Kungiyar, a wata sanarwa, ta ce wani "soja mai bajinta" ne ya kai harin.

An daura wa IS alhakin kai hare-hare na baya-bayan kan Turkiyya wadda ke daukar matakan soji kan kungiyar a kasar Syria da ke makwabtaka da ita.

An rinka alakanta kungiyar masu tada kayar bayan da akalla hare-hare biyu a Turkiyya a shekarar da ta gabata.

Iyalan wadanda aka kashe suna jimami

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Iyalan wadanda aka kashe sun kasance cikin dimuwa

Bayanai na ci gaba da fitowa dangane da harin gidan rawar. Kafofin yada labarai na kasar sun ce dan bindigar da ya kai harin ya harba harsasai akalla 180.

Ya isa wurin cikin motar tasi kafin ya danna ta kofar shiga da wata doguwar bindiga wadda ya dauka daga bayan motar.

Ministan harkokin cikin gidan kasar, Suleyman Soylu, ya tabbatar da cewa an fara farautar dan bindigar.

Ya kara da cewa "muna fatan za a kama maharin nan kusa".