Bama-bamai sun kashe mutum hudu a Somaliya

Kungiyar Al-Shabaab ta sha kai irin wadannan hare-hare
Bayanan hoto,

Kungiyar al-Shabab ta sha kai irin wadannan hare-hare

Wasu motoci dauke da bama-bamai da suka fashe a Mogadishu babban birnin kasar Somaliya sun yi sanadiyyar rasa rayukan akalla mutum hudu.

Mota ta farko ta fashe ne a wajen binciken motoci da ke kusa da sansanin da dakarun kungiyar Tarayyar Afirka suke, yayin da dayar kuma ta fashe a kusa da wani otel.

Kungiyar masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama ta al-Shabab ta dauki nauyin harin.

Al-Shabab ta sha kai irin wadannan hare-hare a birnin da kuma wasu yankunan kasar.

Ana ta jan kafa wajen gudanar da zaben shugaban kasa a Somaliya saboda rashin tabbacin tsaro.