Gambia: An rufe gidan rediyon 'yan adawa

Yahya Jammeh ya shafe shekaru 22 yana mulki a Gambia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yahya Jammeh ya shafe shekaru 22 yana mulki a Gambia

Mahukunta a Gambia sun rufe wani gidan rediyo da ya shahara kuma ya jima yana sukar Shugaban kasar Yahya Jammeh.

Shugaban kungiyar 'yan jaridu na kasar Emil Touray, ya ce jami'an hukumar leken asiri ne suka bayar da umarnin rufe gidan rediyon Teranga FM ba tare da bayar da wani dalili ba.

Wannan ne karon farko da Shugaba Jammeh ke sukar kafafan yada labarai tun bayan da ya ki amincewa da kayin da ya sha a zaben da aka yi a watan da ya gabata.

A shekarar 1994 ne Yahya Jammeh ya hau mulkin kasar, bayan juyin mulkin da ya jagoranta.

Mista Jammeh ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan da ya wuce wanda da farko ya amince da shan kaye a hannun Adama Barrow.

Ya ce ya janye matsayinsa na farko ne bayan la'akari da cewa ba a kidaya kuri'un daidai ba, ya kuma kara da cewa shi ne mutumin da ya lashe zaben da fifikon kuri'a 87,000.

Kungiyar kula da hakkin 'yan jaridu ta duniya ta ce Gambia ce kasa ta 145 a cikin 180 a fannin kula da hakkokin 'yan jarida.

Kazalika kungiyar ta ce akwai barazana a kan duk wani aiki da ya shafi 'yan jarida a kasar.