Mutum 35 sun mutu a Bagadaza, wasu fiye da 60 sun jikkata

Yawancin wadanda suka mutun Leburori ne
Bayanan hoto,

Yawancin wadanda suka mutun Leburori ne

Akalla mutum talatin da biyar ne suka rasa rayukansu sakamakon wani bam da aka dana a cikin wata mota a wani dandali da ke cike da mutane a Bagadaza, yayinda wasu fiye da sittin kuma suka jikkata.

Kungiyar I-S ta ce ita ta kai harin.

Rahotanni sun ce mafi yawan wadanda suka rasa rayukan na su leburori ne da suke jiran fara aiki a birnin Sadr.

Kazalika an rawaito cewa wani bam din da ya tashi a cikin wata motar a kusa da wani asibiti da ke gabashin Bagadazan ya hallaka mutum uku.

Wannan lamari na faruwa ne a dai-dai lokacin da shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya ziyarci dakarunsa da ke zaune a wani sansani a kusa da Bagadaza.

Mr Hollande ya shaidawa dakarun na sa cewa yakar 'yan kungiyar I-S na taimakawa wajen kare hare-haren ta'addanci a kasarsu.