An fara shari'ar mataimakin shugaban Equatorial Guinea a Faransa

Ana zargin Mr Teodorin Obiang da laifin cin hanci da rashawa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ana zargin Mr Teodorin Obiang da laifin cin hanci da rashawa

An fara shari'ar mataimakin shugaban kasar Equatorial Guinea a Faransa bisa zarginsa da laifin cin hanci da rashawa.

Ana zargin Teodorin Obiang Nguema da sayen wani katafaren gida da motocin kasaita a Faransa inda aka ce ya yi amfani da kudin gwamnati wajen yin bushasha.

Mr Obiang wanda da ne a wajen shugaban kasar, ya musanta zargin da ake masa.

Wannan shari'a ita ce ta farko tun bayan da Faransa ta fara binciken shugabannin Afrika a kan mallakar dukiya ba bisa ka'ida ba.

Hakan ya zo ne kusan shekara goma da wata kungiya da ke yaki da cin hanci ta bukaci cewa Faransa ta dauki mataki a kan shugabannin da ake zargi da mallakar haramtattun kudade ko kadarori a Turai.

Cikin abubuwan da Mista Obiang ya mallaka dai har da wani katafaren gida da darajarsa ta kai fiye da dala miliyan dari da kuma manyan motoci na alfarma.

Kungiyar kasashen Afirka ta yamma, ECOWAS, ta bukaci wata kotun kasa da kasa da ta dakatar da sauraron karar, tana mai cewa Mr Obiang na da kariya ta diflomasiyya.

Sai dai kuma kotun ta majalisar dinkin duniya ta yi watsi da bukatar a watan Disamba da ya kare.