Ibrahimovic: Na je Premier ne domin na kunyata marada

Zlatan Ibrahimovic ya ci kwallo 17 a wasa 27 da ya yi tun da ya koma Manchester United a watan Yuli

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ibrahimovic ya ci kwallo 11 a wasa 11 da ya yi wa Manchester United a baya bayan nan

Dan wasan Manchester United Zlatan Ibrahimovic ya ce ya je gasar Premier ne domin ya kunyata masu cewa tasa ta kare a fagen tamaula.

Ibrahimovic, mai shekara 35, ya ci kwallo 17 a wasa 27 tun lokacin da ya koma Man United daga Paris Saint Germain a watan Yuli.

Dan wasan ya ce: "kowace shekara Premier League na kirana in zo, na ki zuwa na ce sai lokacin da kowa yake ganin na kai karshen wasana.

"Sun ce ba abin da zan iya, amma ni kuma kullum kunya nake ba su."

Dan wasan dan kasar Sweden, ya ci kwallo 50 a 2016, inda Lionel Messi ne na Barcelona kawai ya fi shi a cikin shekarar.

In ba domin kwallonsa daya da alkalin wasa Lee Mason, ya hana ba a wasan da suka ci Middlesbrough 2-1 ranar Asabar, da ya kamo Messi.

Ibrahimovic ya ce: "Marada na kara min kuzari sosai.

"Ana biyan masu suka su yi soki-burutsu. Ni kuma ana biyana na taka leda. Yadda nake jin dadin abin kenan."

A ranar Litinin Manchester United za ta je gidan West Ham a wasansu na mako na 20 na Premier (karfe 6:15 na yamma agogon Najeriya).