'Yar Somalia ta zama 'yar majalisa a Amurka

Asalin hoton, AP
Ilhan Omar ta kafa tarihi bayan da ta zamo 'yar Somalia ta farko da aka zaba a matsayin 'yar majalisar dokoki a Amurka.
Ms Omar, wacce aka haifa a Somalia, ta je Amurka ne a matsayin 'yar gudun hijira.
An zabe ta a majalisar wakilai ta jihar Minnesota a wani zabe mai zafi da aka fafata bara.
Zaben Ms Omar, wacce Musulma ce, ya zo kwanaki kadan bayan da zababben Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi 'yan gudun hijirar Somalia a Minnesota da "yada tsattsauran ra'ayi".
Akwai al'ummar Somalia da dama da ke zaune a Amurka, musamman a jihar Minnesota.
Asalin hoton, AP
Da al'Kur'ani aka rantsar da Ilhan Omar
Kuma ana yi wa zaben Ms Omar wani kallon abin da ka iya kara fito da kimar 'yan kasar da ke zaune a jihar da ma Amurka baki daya.
Ilhan Omar ta sha alwashin yin aiki tukuru bayan da aka rantsar da ita.
Wani bidiyo da jaridar Star Tribune, ta wallafa ya nuna Ms Omar tana shan rantsuwa da al-Kur'ani kafin ta gabatar da jawabi a babban birnin jihar.