Nigeria: An sake gano wata 'yar Chibok

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Najeriya na cigaba da farautar 'yan Boko Haram
Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun sake gano wata yarinya daga cikin 'yan matan Chibok fiye da 200 da 'yan Boko Haram suka sace fiye da shekara biyu da ta gabata.
Yarinyar mai suna Rakiya Abubakar, an gano ta ne tare da jaririnta dan wata shida a yankin Alagarno a jihar Borno.
Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta ce yarinyar na samun kulawar jami'an kiwon lafiya kafin a mika ta ga gwamnatin jihar ta Borno.
Ta kara da cewa an gano yarinyar ce a lokacin da ke bincikar wasu da aka kama bisa zargin suna da alaka da Boko Haram.
Fiye da shekara biyu kenan da aka sace yaran su 276 daga makarantarsu a garin Chibok, lamarin da ya ja hankalin duniya sosai.
A watan Oktoban da ya wuce aka sako wasu 21 daga cikinsu bayan wata jarjejeniya da aka cimma da kungiyar ta Boko Haram.
Sai dai har yanzu da dama daga cikinsu na hannun 'ya'yan kungiyar.
A baya-bayan nan dakarun tsaron Najeriya da na makwaftan kasashe na samun nasara kan mayakan Boko Haram.
Amma har yanzu kungiyar na ci gaba da kai hare-hare musamman na kunar bakin wake.
Sai dai rundunar sojin Najeriya ta ce tana na cigaba da farautar 'yan Boko Haram din, kuma a yanzu ta fatattake su daga sansaninsu da ke dajin Sambisa.
Asalin hoton, Getty Images
Sace 'yan makarantar a watan Afrilun 2014 ya ja hankalin duniya sosai