'Akwai bukatar sulhu da mayakan Niger Delta a Nigeria'

Niger Delta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hare-haren na janyo wa Nigeria asarar kudaden shiga

Masana tattalin arziki a Najeriya sun ce tattalin arzikin kasar zai iya bunkasa a 2017 amma bisa sharadin dakatar da fasa bututun mai.

Sun ce kuma za a cimma hakan ne kawai ta hanyar yin sulhu da mayakan sa-kai na yankin Niger Delta mai arzikin man fetur a kasar.

Dr Obadiya Mai Lafiya wanda tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya ne kuma masani kan tattalin arziki, ya ce, idan dai har ba a yi sulhu da tsagerun ba, to babu abin da zai sauya.

Kungiyoyi daban-daban ne dai a yankin na Niger Delta suka rinka fasa bututun mai da na iskar gas da nufin karya tattalin arzikin kasar zagon kasa.

Hakan kuma ya taimaka sosai wajen samun nakasu a kudaden shigar kasar, al'amarin da daga bisani ya janyo karayar tattalin arziki.

Dr Mai Lafiya, ya ce, duk da farashin mai ya daga a kasuwar duniya, idan har ba a zauna da kungiyoyi kamar Niger Delta Avengers ba, to Najeriya ba za ta ci moriyar karin darajar man ba.

Daman dai shugaban Najeriyar, Muhammadu Buhari, a cikin sakonsa na murnar shiga sabuwar shekarar 2017, ya ambaci batun tattaunawa da mayakan.