Mummunar gobara ta yi barna a Chile inda ta kona gidaje

Asalin hoton, ALBERTO MIRANDA
Mummunar gobara ta yi barna a kasar Chile inda ta kona gidaje da dama tare da raunata mutum 19.
Gobarar ta tashi ne a kusa da tsaunin da ke kewayen tashar ruwa ta garin Valparaiso.
Tun daga nesa, za ka iya tsinkayen harsunan wuta da suka kere tsaunukan da ke kewaye da tashar ruwan.
Wutar da ta tashi a wurin, ta lakume kusan gidaje guda 100 abun da ya tilastawa daruruwan jama'a mazauna wurin barin gidajen su.
Tun dai ranar Litinine wutar ta soma,to amma sanadiyar iska mai karfi da zunzuruntun zafi da kuma kekasasshen yanayi, wutar ta yi gargawar bazuwa a ko'ina.
Gwamnatin kasar ta Chile ta ayyana dokar ta baci a yankin baki daya .