'Yanzu muka fara binciken ma'aikatan Bauchi'

An sace mutanen ne a karamar hukumar Ningi
Bayanan hoto,

An ceto mutane 11 a Bauchi

Gwamnatin jihar Bauchi A Najeriya, ta ce za ta ci gaba da gudanar da bincike kan tantance ma'aikata babu kakkautawa domin gano ma'aikatan na bogi.

Hakanne ya sa jihar a baya, ta yi ta kai ruwa-rana da ma`aikatan sakamakon jinkirin biyansu albashi na wata da watanni.

Gwamnan jihar, Mohammed Abdullahi Abubakar ya shaida wa BBC cewa sun shawo kan matsalar rashin biyan albashi, a inda ya ce a yanzu haka ma'aikatan jihar ta Bauchi ba sa bin bashin albashi ko na kobo.

Ya kuma kara da cewa bincike ba zai kare ba, sabo da a kullum wasu ma'aikata na barin aiki wasu kuma su na mutuwa sannan wasu sabbi na kamawa.

Dangane kuma d zargin cewa gwamnatin jihar ta biya ma'aikata albashin ne saboda ziyarar da shugaban kasar, Muhammadu Buhari, ya shirya kaiwa jihar ne, gwamnan ya ce ba gaskiya ba ne.

Ya kuma kalubalanci masu hamayya kan zarge-zargen da suke yi masa wadanda ya ce ba su da tushe ballantana makama.