Ghana: 'Mu kan ji kunya mu ce daga Zango muke'

ghana

Asalin hoton, Getty Images

Da alama rayuwa ba ta da dai ga mazauna yankunan da ake yi wa lakabi da Zango a kasar Ghana.

Mafiya yawan mazaunan wadannan yankuna dai baki ne wadanda suka yi hijra daga wasu kasashen kamar Najeriya da Niger, zuwa Ghana, shekaru da dama.

Sai dai kuma sabanin yankunan asalin 'yan kasar na asali, Zanguna a Ghana ba su da cigaban da ake bukata a irin wannan zamani.

Mataimakin shugaban jam'iyyar MPP reshen birnin Accra, Malam Adam Sabo, ya shaida wa wakilinmu, Muhammad Fahd Adam yanayin da ake ciki a Zango a Ghanar.

"Yau a duk fadin Accra babu wani Zango da za ka samu makarantar sakandare kuma amma sai a rinka cewa ba son yin karatu."In ji Malam Sabo.

Ya kuma kara da cewa " muna fama da matsalar rashin bandaki domin layi ake yi wajen kewayawa."

Dangane kuma da batun tsaftar muhalli, Malam Sabo ya ce "babban abin da ke ci mana tuwo a kwarya kenan."

Wata wadda wakilin namu ya tattauna da ita kan batun ta ce " akwai talauci a Zango sosai har ma idan ka je wani wuri ka ce daga Zango ka ke za ka ga ana yi maka kallon raini."

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Sau uku Nana Akufo-Addo yana tsayawa takara

To sai dai kuma da alama ana gab da magance matsalar domin shugaban kasar mai jiran gado, Nana Akufor-Addo ya yi alwashin inganta rayuwar al'ummar Zango.

Har ma ya ambaci gidauniyar cigaban yankunan mai suna Zango Development Fund.

Duk da cewa mazaunan Zangunan suna cike da farin ciki kan wannan dauki amma akwai masu bayyana fargaba cewa sun gaji da gafara sa ba su ga kaho ba.

'Yan siyasa dai sun sha yin amfani da dimbin kuri'ar yankunan na Zango bisa alkawarin inganta rayuwar mutanen yankunan amma daga karshe sai su yi watsi da su.

Shin ko wannan karon al'amarin zai sauya? Lokaci ne kawai zai tabbatar da hakan.

A watan Janairu ne dai zababben shugaban kasar ta Ghana, Nana Akufor-Addo zai kama aiki.

Shi ne kuma mutumin da ya kayar da shugaban kasar mai ci, John Dramani Mahma, a babban zaben kasar da aka yi a watan Disambar 2016.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

John Dramani Mahama ya amince da faduwa zabe