Jakadan Burtaniya a EU ya yi murabus

Ya ce Burtaniya za ta dandana kudarta kan ficewa daga EU
Bayanan hoto,

Sir Ivan Rogers ya ce a fadi gaskiya komai dacinta

Jakadan Burtaniya a Tarayyar Turai, EU, Ivan Rogers ya yi murabus daga kujerarsa.

A wata wasika da ya sanar da murabus din ta bazata, ranar Talata, mista Rogers, ya kuma ja gargadi ma'aikata da su kalubalanci duk wani tunanin da bai dace ba kan ficewar Burtaniya daga EU.

Ya kara da jan hankalin ma'aikatan da ka da su sassauta wajen fadin gaskiya komai dacinta.

Har wa yau, mista Rogers ya ce Burtaniya ba ta da wakilan kwararru da suke wakiltar ta a Tarayyar Turai.

Da ma dai Sir Ivan ya fuskanci suka bisa fadin cewa Burtaniyar za ta kwashe fiye da shekara goma kafin ta cimma yarjejeniyar kasuwanci da EU.