Fitacciyar mawakiya Janet Jackson ta haihu

Janet Jackson da mijinta, Wissam al-Mana

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Janet Jackson da mijinta Wissam al-Mana

Mai magana da yawun Janet Jackson ya ce mawakiyar 'yar kasar Amurka ta haifi da namiji tana da shekara 50 a duniya.

Wata sanarwa da aka fitar ta ce mawakiyar da mijinta, dan kasuwar nan na kasar Qatar, Wissam Al Mana, na farin cikin samun jaririn da suka rada wa suna, Eissa Al Mana.

Sanarwar ta kara da cewa,"Janet ta haihu lafiya lau kuma yanzu haka tana hutawa."

A watan Afrilun da ya wuce ne aka yi ta rade-radin cewa mawakiyar tana da juna-biyu bayan ta dage tafiye-tafiyen gabatar da wakoki da za ta yi.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ba Janet Jackson ce mawakiya ta farko da da haihu bayan shekarunta sun ja ba

A wancan lokacin, ta wallafa sakon bidiyo a shafinta na Twitter inda ta shaida wa masu sha'awar wakokinta cewa ta dage tafiye-tafiyen ne saboda "wani abu da ya zo mata bagatatan".

A cewarta, "Ina ganin yana da matukar muhimmanci na sanar da ku. Ina rokon ku da ku fahimci halin da nake ciki."

Mrs Jackson ta ce tana son ta mayar da hankali wajen goyon-ciki tun bayan aurenta a shekarar 2012.