Myanmar ta ce babu shaidar an yi wa Musulmi kisan kiyashi

Musulmin Rohingya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Musulmi 'yan kabilar Rohingya suna tsere wa zuwa kasar Bangladash domin guje wa rikicin

Wani kwamitin bincike a Myamar ya ce har yanzu bai samu wata hujja da ke nuna cewa an yi wa musulman kasar 'yan kabilar Rohingya kisan kiyashi a jihar Rakhine ba.

A rahotonsa na wucin-gadi, kwamitin ya ce babu isasshiyar hujjar da ta tabbatar da zarge-zargen cewar fyade ya zama ruwan-dare a yankin.

Sai dai kwamitin bai ce komai ba a kan zarge-zargen da aka yi wa jami'an tsaro na kashe mutane.

An yi ta rade-radin cewar ana musguna wa 'yan kabilar Rohingya tun lokacin da sojojin kasar suka fara yaki da 'yan tada-kayar-baya a watan Oktoban da ya wuce.

Wasu sun bayyana matakin dakarun kasar a matsayin kisan kare-dangi, jogarar kasar ta Myanmar, Aug San Suu Kyi, ta fuskanci suka daga kasashen duniya.

Kwamitin, wanda wani tsohon sojan kasar Janar Myint Swe ke jagoranta, zai kammala rahotonsa kafin karshen watan Janairu.

Kwamitin ya ce har yanzu akwai musulmai 'yan kabilar Rohingya wadanda suke zama a Rakhine kuma ba a lalata masallatai da makarantu ba.