An samu sojan Isra'ila da laifin kashe Bafalasdine

Masu gangami

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

An yi gangami a Tel Aviv domin nuna goyon bayan sojan

Wata kotu a Isra'ila ta samu wani sojan kasar da laifin harbe wani Bafalasdine ba da niyya ba, bayan an jikkata shi.

Sajan Elor Azaria, dan shekara 20, ya bindige bafalasdine Abdul Fatah Al-Sharif a ka lokacin da yake kwance magashiyan a kan titi.

Lamarin ya faru ne a yankin Hebron da Isra'ila ta mamaye a gabar yamma da kogin Jordan cikin watan Maris, bayan Bafalasdinen ya caka wa wani soja wuka.

Sajan Azaria ya ce ya yi zaton maharin ya yi damara da rigar bam ne, amma masu shigar da kara sun ce manufarsa ita ce yin ramuwar gayya.

Wakiliyar BBC a Tel Aviv, Yolande Knell, ta ce shari'ar ta janyo rarrabuwar kai a Isra'ila.

An gudanar da zanga-zanga don nuna goyon baya ga sojan, sai dai manyan hafsoshin sojan Isra'ila sun yi saurin cewa abin da Sajan Azaria ya aikata ya saba da akidun rundunar tsaron Isra'ila.