Ma'aikata mata na hutun kwana daya saboda jinin al'ada a Zambia

Wasu matan a Zambia ba sa son hutun jini al'adar da ake bayarwa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wasu matan a Zambia ba sa son hutun jini al'adar da ake bayarwa

A kasar Zambia, an samar da wata doka da ba kasafai ake ganin irin ta ba da ake amfani da ita a inda a kowanne wata ma'aikata mata su na da kwana daya da ake ba su hutu a lokacin da suke yin jinin Al'ada.

Ana kuma kiran wannan rana da suna "Mothers Day" a turance.

Cikin ka'idar dokar ba sai lallai mace ta na da aure ko ta na da 'ya'ya ba kafin a bata ranar hutun, duk wata mace in dai ita ma'aikaciya ce za ta ci moriyar wannan shiri.

Haka kuma ana gurfanar da duk wani shugaban ma'aikata da ya hana ma'aikatan sa mata ranar hutun gaban kuliya dan fuskantar hukunci.

Dokar dai ta zama abin tattaunawa a tsakanin jama'a a cikin kasar ta Zambia, in da wasu ke ganin ta yi dai-dai, wasu kuwa na ganin ba ta yi ba.

Kazalika a bangaren su ma ma'aikata matan, wasunsu na son wannan hutu, wasu kuwa na ganin ba sa bukatarsa.