Majalisar dattawa za ta yi bincike a kan rikicin Kaduna

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i
Bayanan hoto,

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i

Majalisar dattawan Najeriya ta ce za ta gudanar da bincike a kan musabbabin rikicin da ake fama da shi a kudancin jihar Kaduna da nufin samar da maslaha.

Wasu daga cikin al`umomin yankin dai sun ba da shawarar cewa ya kamata a yi amfani da shawarwarin da wasu kwamitoci suka ba wa wasu gwamnatocin da aka yi a jihar a baya, maimakon a kwashe wani lokaci ana yin sabon bincike.

Senata Shehu Sani dan majalisar dattawa ne daga jihar Kaduna, ya kuma shaidawa BBC cewa,an gabatar da wani kuduri a gaban majalisar wanda ya nemi ayi bincike domin a gano wadanda suke da hannu a kan wannan rikici, sannan kuma a gano wadanda rikicin ya shafa, da kuma fito da hanyoyi na tsaro ta yadda za a magance afkuwar irin wadannan tashe-tashen hankulan a gaba.

Sanata Shehu Sani, ya kuma ce za a duba aga irin taimakon da gwamnati za ta yiwa wadanda irin wannan rikici ya shafa.

Wannan ne dai karon farko da majalisar dattawan za ta shiga cikin wannan batu domin ganin an kawo karshen wannan rikici da ke faruwa a kudancin Kaduna.