Kasar China za ta bai wa mutum miliyan 13 aikin yi

China

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sama da mutane miliyan dari ke rubuta jarrabawar ko wace shekara

Gwamnatin China za ta kirkiro wa mutane fiya da miliyan 13 aikin yi cikin shekara biyar ta hanyar zuba jari a harkar makamashin da ba ya gurbata muhalli.

Hukumomin kasar sun ce za su sanya biliyoyin dalar Amurka don wannan shiri.

China ta ce tana mayar da hankali wajen samar da tsabtacen makamashi.

Za a yi hakan ne cikin gaggawa sakamakon yadda makamashin kwal yake gurbata muhalli a kasar.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Shugaban kasar China Xi Jinping yana son mai da hankali a kan makamashin da ba ya gurbata muhalli

Ko a makon da ya gabata, wani hayaki da ya gurbata iska ya rika shake mutane a gabashin kasar.

Wakilin BBC a Beijing ya ce duk da cewa kudin da China za ta kashe dala billiyan 360 makudan gaske ne, amma ba zai yi tasiri ba ganin yadda bukatun kasar suke da yawa.

Makamashin da za a samar zai kasance kashi 15 kawai cikin 100 na abin da kasar ke bukata a cikin shekara biyar.