Riyad Mahrez na Algeria ne gwarzon Afirka na 2016

Kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka
Bayanan hoto,

Mahrez ne ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na BBC a watan Disamba

Dan wasan gaba na Algeria Riyad Mahrez shi ne ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afirka na CAF na 2016.

Mahrez wanda ya ke yi wa Leicester City wasa a gasar Premier ya taka muhimmiyar rawa a kofin gasar Premier da kungiyar ta dauka a kakar da ta wuce, inda ya ci musu kwallo 17.

A watan Disambar da ya gabata, Mahrez ya samu kyautar gwarzon dan wasan Afirka na BBC na 2016.

A bangaren mata kuwa, Asisat Oshoala 'yar Najeriya ita ce ta zama gwarzuwar 'yar wasan kwallon kafa ta Afirka ta 2016 ta CAF.

An gudanar da bikin raba kyautukan ne a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

A shekarar 2015 dai Pierre-Emerick Aubameyang ne ya lashe kyautar ta CAF.

Kyautar gwarzon dan kwallon Afirka ta 2016

1. Riyad Mahrez (Algeria da Leicester City) - Kuria 361

2. Pierre-Emerick Aubameyang (Gabon da Borussia Dortmund) - Kuria 313

3. Sadio Mane (Senegal da Liverpool) - Kuria 186 votes

Gwarzon dan kwallon Afirka mai taka-leda a Afirka

1. Denis Onyango (Uganda da Mamelodi Sundowns) - Kuria 252

2. Khama Billiat (Zimbabwe da Mamelodi Sundowns) - Kuria 228

3. Rainford Kalaba (Zambia da TP Mazembe) -Kuria 206

Macen da ta fi kwazo a 2016

Asisat Oshola (Nigeria da kungiyar mata ta Arsenal )

Bayanan hoto,

Daga Hagu: Pierre-Emerick Aubameyang sai Riyad Mahrez sai Asisat Oshola da kuma Sadio Mane

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Matashin dan kwallo mai tashe

Kelechi Iheanacho (Nigeria da Manchester City)

Matashin dan wasan da ya taka rawa

Alex Iwobi (Nigeria da Arsenal)

Mai horor da tamaula da babu kamarsa

Pitso Mosimane (Mamelodi Sundowns)

Kungiyar tamaula da ta fi fice

Mamelodi Sundowns

Tawagar kwallon kafa da ta taka rawar gani

Uganda

Tawagar kwallon kafa ta mata da ta taka rawar a 2016

Super Falcons ta Nigeria

Alkalin wasan kwallon kafa da babu kamarsa

Bakary Papa Gassama (Gambia)

Shugaban kwallon kafa da babu kamarsa

Manuel Lopes Nascimento, shugaban hukumar kwallon kafa ta Guinea Bissau

'Yan mazan jiya a kwallon kafar Afirka

Laurent Pokou - Tsohon dan kwallon Cote d'Ivoire, wanda ya mutu a watan Nuwambar 2016

Emilienne Mbango - Kamaru

Kyautar mai masaukin baki

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari

'Yan wasan Afirka 11

Mai tsaron bayar: Denis Onyango (Uganda da Mamelodi Sundowns)

Masu tsaron baya: Serge Aurier (Cote d'Ivoire da Paris Saint-Germain), Aymen Abdennour (Tunisia da Valencia), Eric Bailly (Cote d'Ivoire da Manchester United), Joyce Lomalisa (DR Congo da AS Vita)

Masu buga tsakiya: Khama Billiat (Zimbabwe da Mamelodi Sundowns), Rainford Kalaba (Zambia da TP Mazembe), Keegan Dolly (South Africa da Mamelodi Sundowns),

Masu cin kwallo: Pierre-Emerick Aubameyang (Gabon da Borussia Dortmund), Sadio Mane (Senegal da Liverpool), Riyad Mahrez (Algeria da Leicester City)

Masu jiran kar-ta-kwana

Aymen Mathlouthi (Tunisia da Etoile du Sahel), Kalidou Koulibaly (Senegal da Napoli), Salif Coulibaly (Mali da TP Mazembe), Islam Slimani (Algeria da Leicester City), Mohamed Salah (Masar da Roma), Kelechi Iheanacho (Nigeria da Manchester City), Alex Iwobi (Nigeria da Arsenal)