Nigeria: PDP ta zargi APC da yi mata bita da kulli a kan bude hedkwatarta a Abuja

PDP ta sha zargin APC da yi mata ba dai-dai ba
Babbar jam`iyyar adawar Najeriya, wato PDP ta zargi jam`iyyar APC mai mulki cewa ita ce ta ke kitsa makirci wajen hana bude mata hedikwatarta da ke Abuja, babban birnin kasar.
PDP ta ce APC na yin haka ne domin hana mata natsuwa wajen yin hamayya da ita.
Sai dai jam`iyyar APC a nata bangaren ta musanta, ta na cewa radadin faduwar zabe ne ke gigita PDP.
Tun a watan mayun bara ne rundunar `yan sandan Najeriya ta rufe hedkwatar PDP sakamakon fargabar cewa bangarorin jam`iyyar za su gwabza fada a kan sakatariyar.