Donald Trump ya sake musanta kutsen da aka zargi Rasha da yi a Zabe

Donald Trump na ganin sam Rasha ba ta aikata abinda ake zarginta da aikatawa ba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Donald Trump na ganin sam Rasha ba ta aikata abinda ake zarginta da aikatawa ba

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya sake nuna shakku a kan zargin da ake na cewa Rasha ta yi katsalandan a zaben Amurka da aka yi a shekarar da ta gabata.

Ka Mr Trump ya yi a shafin Twitter sun zo ne sa'oi kafin jami'an leken asirin Amurka su yi masa karin haske kan dalilin da ya sa su ka yi imanin cewa Rasha ta umarci masu kutse a shafin intanet da su yi wa abokiyar hamayyarsa ta jam'iyyar democrats Hillary Clinton zagon kasa a lokacin zaben.

A martanin da ya mayar, mataimakin shugaban kasar Joe Biden ya ce matukar rashin hankali ne ga Trump ya ce yana shakku kan wani abu da jami'an hukumar leken asirin kasar suka fada.

Tuni dai shugana Obama ya karbi rahoton hukumomin wanda ya ce manyan jami'an gwamnatin Rasha sun cashe da suka samu labarin cewa Trump ya samu nasara a zaben.