John Obi Mikel ya koma kulob din China

Obi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kulob din Chelsea ya ki sanya Obi a wasa a kakar wasanni ta bana

Dan wasan Chelsea da ke buga wa Nigeria wasan tsakiya John Obi Mikel ya koma kulob din Tianjin Teda na kasar China.

Obi ne dan wasa na baya bayan nan da ya bar kulob din Turai ya koma kasar ta China.

A ranar Alhamis ne aka yi wa dan wasan gwaji domin tabbatar da lafiyarsa a birnin Beijing, kuma a ranar Juma'a hukumar kwallon kafar Asia ta tabbatar da cewa Obi ya koma China.

Dan wasan mai shekara 29 bai buga wa Chelsea wasa ko da sau daya ba a kakar wasan da muke ciki saboda ya buga wa Najeriya wasan cin kofin Afirka.

Mikel Obi ya shafe fiye da shekara goma a Stamford Bridge, kuma yanzu sabon kulob dinsa zai rika biyan sa $173,432 a kowanne mako, a cewar kafafen watsa labaran China.

Mikel na cikin tawagar da ta ci wa Chelsea kofin zakarun Turai guda daya da na gasar Premier guda biyu da kuma na FA guda hudu.

Kulob-kulob din China sun sayi manyan 'yan wasa a 'yan watannin nan cikin su har da dan wasan Argentina Carlos Tevez wanda ya koma Shanghai Shenhua a kan $87.65m.

A makon jiya ma, dan wasan Brazil Oscar ya koma Shanghai SIPG daga Chelsea a kan Yuro 60m.