'Nigeria za ta fuskanci matsala idan ta rufe filin jirgin Abuja'

An soki matakin rufe filin jirgin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kamfanonin jiragen sama da 'yan kasuwa sun soki matakin rufe filin jirgin

Kungiyar masu kamfanonin jiragen sama a Najeriya ta cewa akwai yiwuwa a fuskanci cikas a zirga-zirgar jiragen sama da zarar gwamnatin tarayya ta rufe filin jirgin saman Abuja.

A watan jiya ne dai ma'aikatar kula da sufurin jiragen saman kasar ta ce za a rufe filin tsawon makonni shida domin a yi gyare-gyaren a tituna.

Ta ce za a karkatar da tashi da kuma saukar jiragen saman zuwa Kaduna.

Sai dai wani babban jami'in jiragen sama na Arik Airline, Captain Ado Sanusi, ya shaida wa BBC cewa koda yake suna goyon bayan matakin amma suna so a yi taka-tsantsan.

Ya kara da cewa, "Yawancin lokuta idan an ce za a yi gyaran filin jirgin sama na wata uku zuwa hudu yana kai wa shekara daya zuwa biyu. Kuma anya Kaduna tana da wurin da za a iya ajiye man jirgin sama? Mun yi magana da masu ba mu man jirgi kuma sun ce Kaduna ba ta da karfin da za ta iya ajiye mai da yawa."

Captain Sanusi ya nemi gwamnati ta sake duba wannan mataki, yana mai cewa a kullum suna sauke jirage sama da 80 a Abuja kuma ba su da tabbacin cewa filin jirgin saman Kaduna zai iya daukar wannan dawainiya.

Da ma dai wasu masu ruwa da tsaki a sufurin jiragen saman na fargabar sauke fasinjoji a Kaduna, musamman ganin cewa hanyar Abuja zuwa Kaduna na fama da barayin mutane domin karbar kudin-fansa.

Sai dai ministan sufurin jiragen saman Hadi Sirika ya ce za su dauki matakan tsaro a kan hanyar, yana mai cewa gyara titin jirgin saman na Abuja na da matukar muhimmanci.