An gano kawunan fursunoni 31 a fille a wani gidan yari da ke Brazil

'Yan sanda sun yi curko-curko a gefen titin da gidan yarin ya ke

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

'Yan sanda sun yi curko-curko a gefen titin da gidan yarin ya ke

Wani gungun 'yan daba da ke da rassa a mafi yawancin gidajen yarin kasar Brazil sun fille kawunan wasu fursunoni da dama a wani gidan yari da ke arewacin jihar Roraima.

Wannan shi ne karo na biyu da irin wannan ta'asa ta afku a kasa da mako guda.

Mahukunta sun yi amanna cewa fille kawunan da aka yi ya faru ne sakamakon wani fada tsakanin 'ya'yan kungiyar 'yan daban ta PCC a gidan yarin da ke da cunkoson jama'a da ke babban birnin jihar Boa Vista.

An dai gano gawawwaki 31 yawancinsu an fille musu kai.

Wani jami'in gwamnatin Brazil ya fada wa BBC cewa a yanzu an shawo kan lamarin, kuma babu wani fursuna da ya tsere.