Bikin rantsar da sabon shugaban Ghana ya kankama

Magoya bayan shugaban Mahama da na Akuffo Addo a tare.
Bayanan hoto,

Mr. Addo ya lashe zabe ne bayan yin takara har sau hudu

Kasar Ghana ta shirya tsaf domin bikin rantsar da Nana Akuffo Addo a zaman shugaban kasar na 12 a tarihi kuma na 5 a jamhuriya ta hudu.

Da misalin karfe 10 na safiyar yau Assabar agogon kasar ne za a rantsar da sabon shugaban a yayin wani gagarumin biki a Accra babban birnin kasar.

Hakan ya biyo bayan da Nana Akuffo Addo - wani lauya mai fafutukar kare hakkin bil'adama - ya kayar da shugaba mai-ci John Dramani Mahama a zaben da aka gudanar a watan jiya.

Shugabannin kasashen Afrika 11 ne ake sa ran za su halarci bikin ranstuwar, wanda zai gudana a dandalin Independence Square da ke birnin na Accra.