Sabon shugaban Ghana ya sha rantsuwar kama aiki

Bikin rantsuwa
Bayanan hoto,

An bude sabon babin siyasa a Ghana

An rantsar da Nana Akufo-Addo a matsayin shugaban kasar na 12 a tarihi kuma na biyar a jamhuriya ta hudu.

Mr Addo ya sha rantsuwa ne a gaban wasu shugabannin kasashen Afirka a Accra, babban birnin kasar da misalin karfe 11 a agogon Ghana, wato karfe 12 a agogon Najeriya da Nijar.

Sabon shugaban kasar ta Ghana ya sha alwashin yaki da cin hanci da rashawa tare da samar wa matasa ayyuka.

Kazalika Mr Addo ya yi alkawarin bayar da ilimi kyauta da kuma farfado da masana'antun kasar wadanda suka durkushe, koda yake masu sukar sa sun ce da wuya ya iya aiwatar da shirin nasa.

Nana Akufo-Addo, mai shekara 72, lauya ne mai fafutukar kare hakkin bil adama - kuma sau biyu yana shan kaye a zaben shugaban kasar, inda ya yi nasara a karo na uku.

An zabe shi ne a karkashin jam'iyyar New Patriotic Party.

Bayanan hoto,

Dubban mutane ne suka halarci bikin rantsar da Nana Akufo-Addo

Bayanan hoto,

Ghana ta yi nisa a turbar dimokradiyya