Wanene sabon shugaban Ghana Nana Akufo-Addo?

  • Nasidi Adamu Yahya
  • BBC Hausa
Matasa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Matasan kasar Ghana na fama da rashin aiki

An haifi sabon shugaban kasar Ghana, Nana Dankwa Akufo-Addo ranar 29 ga watan Maris din shekarar 1944, a unguwar da ake kira Swalaba, da ke tsakiyar birnin Accra.

Akufo-Addo da ne ga Edward Akufo-Addo, wanda ya shugabanci kasar Ghana daga shekarar 1969-72; wanda kuma shi ne ministan shari'a na uku a jerin ministocin ma'aikatar shari'ar kasar.

Sabon shugaban na Ghana ya yi makarantar Firamarensa ne da kuma sakandare a birnin Accra.

Daga bisani ya tafi Ingila inda ya fara karatu a fannin fasaha, a jami'ar Oxford, amma daga bisani mahaifinsa ya cire shi daga makarantar.

Ya koma kasar Ghana a shekarar 1962, inda ya koyar a makarantar da ake kira Accra Academy, kuma daga bisani ya shiga jami'ar Ghana a shekarar 1964, ya karantar a fannin tsimi da tanadi.

Bayan haka ne ya koma Burtaniya, inda ya karanci aikin lauya, kuma an rantsar da shi a matsayin lauyan Ingila a shekarar 1971; kazalika an rantsar da shi a matsayin lauyan Ghana a shekarar 1975.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Nana Akufo-Addo ya fito ne daga tsatson siyasa

'Takarar shugabancin kasa'

Akufo-Addo ya yi aikin lauya a birnin Paris na Faransa, tsawon shekaru biyar.

Ya koma kasar Ghana a shekarar 1975, inda ya ci gaba da gudanar da aikin lauya, da kare hakkin bil adama da fafutukar tabbatar da mulkin dimokaradiyya.

Taken Akufo-Addo da jam'iyarsa ta NPP shi ne kawar da cin hanci da rashawa.

Akufo-Addo mutum ne da ke da sha'awar wasanni, musamman na kwallon kafa, da karance-karance, da sauraron wakoki.

Nana Akufo-Addo ya auri Rebecca Akufo-Addo, kuma Allah ya albarkace su da 'ya'ya biyar mata, da jikoki guda biyu.

Akufo-Addo ya shiga harkokin siyasa gadan-gadan, inda aka zabe shi sau uku a matsayin dan majalisar dokokin kasar tsakanin shekarar 1996 da 2004.

Haka kuma tsakanin shekarar 2001 zuwa 2007, ya zama ministan shari'a kuma Antoni-Janar; kana ya zama ministan harkokin waje tsawon shakaru biyar a gwamnatin tsohon shugaban kasar John Kufuor.

Akufo-Addo ya yi murabus daga gwamnatin a watan Yulin shekarar 2007, domin ya yi takarar shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar da ke mulki a wancan lokacin, New Patriotic Party (NPP), a zaben shekarar 2008.

'Kawar da cin hanci da rashawa'

A zagaye na farko na zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar 7 ga watan Disambar shekarar 2008, Akufo-Addo ya samu kuri'u fiye da na abokin hamayyarsa, John Atta Mills; sai dai bai samu kashi hamsin cikin dari da ake bukata don lashe zaben ba.

Sai dai zagaye na biyu, Mills ya samu kashi 50.23% na kuri'un, shi kuwa Akufo-Addo ya samu 49.13%, abin da ya sa Mills din ya lashe zaben shugaban kasar.

A watan Agustan shekarar 2010, jam'iyyar NPP ta zabi Nana Akufo-Addo don zama dan takarar shugabancin kasar a zaben da za a yi ranar bakwai ga watan Disambar shekarar 2012.

Ya samu kashi 79 cikin dari na kuri'un da wakilan da ke zabar wanda zai yi wa jam'iyyar takarar shugabancin kasa suka kada, a lokacin babban taron jam'iyyar.

Sai dai ya sha kaye a hannun John Dramani Mahama a zaben shugaban kasar na shekarar 2012.

An sake tsayar da Akufo-Addo a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NPP a zaben da aka yi a watan Disambar da ya gabata, inda ya kasance mutum na farko da ya kayar da shugaba mai-ci.

An rantsar da Mr Akufo-Addo ranar Asabar bakwai ga watan Janairu na shekarar 2017.

Taken Akufo-Addo da jam'iyarsa ta NPP shi ne kawar da cin hanci da rashawa.

Akufo-Addo mutum ne da ke da sha'awar wasanni, musamman na kwallon kafa, da karance-karance, da sauraron wakoki.

Nana Akufo-Addo ya auri Rebecca Akufo-Addo, kuma Allah ya albarkace su da 'ya'ya biyar mata, da jikoki guda biyu.