PDP ta yi Allah wadai da korar 'yan sanda 6 a Najeriya

Nigeria PDP

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jam'iyyar adawa a Najeriya ta PDP

A Najeriya, jam'iyyar adawa ta PDP ta yi Allah wadai da matakin da rundunar 'yan sandan kasar ta dauka na sallamar jami'anta shida dake aiki da gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike.

A cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Prince Dayo Adeyeye ya fitar, jam'iyyar PDP ta ce shari'ar da aka yi wa 'yan sandan a asirce, da kuma sallamarsu da aka yi, abu ne na rashin gaskiya.

Jam'iyyar ta yi zargin cewa, saurin korar 'yan sandan da aka yi, wata karin alamace ga yunkurin yin magudi da halaka gwamna Wike gabanin zaben cike gurbi da aka gudanar a jihar Rivers a watan Disamba.

Jam'iyyar PDP ta ce "gwamnatin APC ta yanke shawarar hukunta jami'an 'yan sandan ne saboda sun dage yin aikinsu yadda ya kamata, sun ki aiwatar da shirin wasu na ganin bayan gwamna Wike".

Ta kuma kara da cewa zargin saba ka'idojin aiki da ake wa 'yan sandan, wani abin kunya ne ga tsarin aikin dan sanda da tafarkin dimukradiyya.

A saboda haka jam'iyyar ta PDP ta yi kiran ganin an mayar da 'yan sandan bakin aikinsu ba tare da bata lokaci ba, domin kare martabar aikin, da gaskiya da adalci.

Asalin hoton, Nigerian government

Bayanan hoto,

Sufeto Janar na 'yan sanda Idris Ibrahim ya sha alwashin kawo sauyi a hukumar

In za a tuna, rundunar 'yan sandan Najeriya ta sallami jami'an na ta shida ne wadanda ta ce sun aikata laifuka daban-daban a lokacin zaben 'yan majalisu da aka gudanar a jihar Rivers.

Kakin rundunar Don Awunah ya ce bincike ya nuna cewa jami'an wadanda suka hada da Sufeto Eyo Victor da Sajen Peter Ekpo da Sajen Ogoni Goodluck sun yi harbi cikin jama'a ba bisa ka'ida ba.

Sauran sun hada da Sajen Orji Nwoke da Sajen Okpe Ezekiel da kuma Sajen Tanko Akor.

Ta kara da cewa sun aikata laifin ne ranar 10 ga watan Disambar 2016 lokacin da suka bi tawagar Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike, wajen dirar mikiya a kan sakatariyar karamar hukumar Fatakwal.