Kalubalen da ke gaban Nana Akufo-Addo

  • Haruna Shehu Mjos
  • BBC Hausa
Ghana

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masu rawar gargajiya a wurin rantsar da sabon shugaban Ghana

Sabon shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya ce bayan shekaru kusan 60 da samun 'yancin kai, kasar ba ta da wani uzuri na talaucewa.

A jawabinsa yayin da ake rantsar da shi a yau, Nana Akufo-Addo ya sha alwashin rage kudaden haraji da nufin bunkasa tattalin arzikin kasar.

Ya kuma yabawa magabacinsa, John Dramani Mahama, bisa yadda ya amince da shan kaye a zaben watan jiya cikin mutunci.

Saurari rahoton wakilinmu a Ghana, Mohammed Fahad Adam:

Bayanan sauti

Kalubalen dake gaban Nana Akufo-Addo

Wasu daga cikin alkawuran Mista Akufo-Addo

  • Sabon shugaban ya sha alwashin bunkasa harkokin aikin gona da kasuwanci a kasar.
  • Sabon shugaban ya kuma yi alkawarin rage kudin haraji a kasar da nufin bunkasa tattalin arziki, wani abu da 'yan kasuwa suka yi maraba da shi.
  • Kazalika, Mista Nana Akufo-Ado ya yi alkawarin yin tsantsani da taka tsantsan wajen kashe kudaden gwamnati, yana mai cewa aikin gwamnati, ba hanya ba ce ta tara dukiya.

Kalubalen da zai iya fuskanta

Ana gani yunkurin sabon shugaban na rage kudin haraji, zai iya sa ya fuskanci kalubale a wurin hukumar bayar da lamuni ta duniya IMF.

Ghana dai, daya ce daga cikin kasashen da suka fi naman cocoa da hada-hadar zinari, kuma saboda matsalolin basussuka da hauhawar farashin kayayyaki, kasar ta shiga wani shiri na hukumar bayar da lamuni na duniya IMF da nufin farfado da tattalin arzikinta.

Saboda, ana gani babu tabbas ko sabon shugaban zai iya ci gaba da rage kudin harajin, sannan a gefe daya kuma, ya yi aiki da matakan tsuke bakin aljihu na IMF don kasar ta ci gajiyar tallafin dala miliyan 918 daga IMF.