Mara wayau ne kadai zai soki alaka da Rasha— Trump

Trump

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump da shugaba Putin na Rasha

Shugaban Amurka mai jiran gado, Donald Trump, ya ce kulla kyakkyawar dangantaka da Rasha, abu ne mai kyau, yana mai cewa, marasa wayau ne kawai za su yi tunani hakan bai da kyau.

A wani rubutua shafinsa na twitter, Mista Trump ya ce idan ya kama aiki a matsayin shugaban kasa, Rasha za ta mutunta Amurka fiye da yadda take yi yanzu.

A jiya Juma'a jami'an hukumomin leken asiri na Amurka suka fitar da wani rahoto, inda suka ce shugaban Rasha Vladimir Putin ne da kansa, ya bayar da umurnin kutsen da aka yi wa Amurka don taimaka wa Mista Trump cin zabe.

Wakilin BBC a Washington ya ce Mista Trump zai iya fuskantar gayyata, don ya kare batun kutse da ake zargin Rasha da yi, wanda ake gani wata babbar barazana ce a Amurka.