Nigeria: Masu fataucin lemon zaki sun shiga yajin aikin sai baba ta gani

Yajin aikin masu fataucin lemon ya shafi bangarori da dama
Bayanan hoto,

Yajin aikin masu fataucin lemon ya shafi bangarori da dama

A Najeriya, masu fataucin lemo daga jihar Binuwai zuwa sassan kasar sun fara wani yajin aiki na sai baba ta gani, don nuna rashin jin dadinsu game da tilasta musu biyan haraji barkatai.

Kungiyar masu fataucin lemon ce ta bukaci `ya`yanta su shiga yajin aikin da nufin jan hankalin mahukuntan jihar Binuwai domin su share musu hawaye.

Masu fataucin lemon dai sun bayyana cewa ba su da wata matsala tsakaninsu da gwamnatin Binuwai dangane da asalin harajin da ake karba a hannunsu a hukumance, amma abinda ya fi damunsu shi ne zargin da suke na yadda wasu gungun mutane ke fito da wasu tsarabe-tsarabe ana cin zalinsu.

Kungiyar ta ce ana rubanya harajin da yakamata a karba daga hannayensu.

Wannan yajin dai ya haddasa karanci, da kuma tsadar lemo a Abuja da ma wasu bangarorin Najeriya da dama, inda masu kasa kayan marmari a bakin tituna ke cewa farashin lemon ya tashi dan haka ba za su iya siya ba domin ba bu riba.

A bangare guda kuma, suma masu shan lemon zakin sun koka game da karancinsa da ma tsadarsa.

A nata bangaren, gwamnatin jihar Binuwai ta ce ta na da labarin bata garin da ke zaluntar masu fataucin lemon da sunan haraji, kuma har ma rundunar 'yan sandan jihar ta kama mutum sama da 80 da nufin hukuntawa.

A hannu guda kuma, gwamnatin tarayyar na sa ran tattaunawa da shugabannin kungiyar masu lemon da nufin sulhuntawa a wannan makon.