Nigeria: 'Yan matan Chibok 276 sun cika kwana 1000 da sacewa

Mayakan Boko Haram sun sha sace mutane da suka hada da mata da yara

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mayakan Boko Haram sun sha sace mutane da suka hada da mata da yara

A ranar Lahadi ne ake cika kwanaki 1000 da sace 'yan matan makarantar Chibok 276 da mayakan Boko Haram suka yi a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nigeria.

Lamarin dai ya ja hankalin mutane da gwamnatoci a sassan duniya daban-daban; inda aka yi ta yin zanga-zangar neman a sako su.

Fiye da 'yan mata 50 ne suka kubutar da kansu tun ranar da aka sace sun wato 14 ga watan Afrilun 2014, yayin da kawo yanzu gwamnati ta samu kwato wasu kari 23.

A cikin wata sanarwa da ta fitar kan cika kawanakki dubun da sace su, kungiyar kare hakkin biladama ta Amnesty International ta yi kira ga gwamnatin Najeriyar ta kara matsa kaimi wajen ganin ta kubutar da sauran 'yan matan, da ma wasu da ke hannun mayakan.

Kungiyar ta Amnesty ta kuma yi kira ga kungiyar Boko Haram da ta kawo karshen ukubar da ta jefa 'yan matan dama sauran wadanda take rike da su, don su koma cikin iyalansu.

Amnesty ta cigaba da cewa, ba wai ta na zargin gwamnati da rashin kokari wajn kubuto da 'yammatan da ma sauran wadanda aka sace ba ne,ta na so ne a kara himma saboda ba yammatan kadai ne a hannun mayakan ba, har ma da wasu mutane da suka hada da mata da yara.

Sai dai tace tana yaba wa gwamnatin kasar kwarai da gaske wajen kubutar da sauran.