Djokovic ya doke Murray a Qatar Open

Kwallon tennis

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Andy Murray ne ya lashe gasar Qatar Open

Novak Djokovic ya lashe gasar kwallon tennis ta Qatar ta bana, bayan da ya doke Sir Andy Murray a wasan karshe da suka kara a ranar Asabar.

Djokovic ya yi nasara a kan Murray da ci 6-3 5-7 6-4 wanda hakan ya sa aka takawa dan Burtaniya burki kan yawan lashe wasanni 28 da ya yi a jere.

Sai dai kuma duk da hakan Murray yana nan a matakinsa na daya a jerin wadanda suke kan gaba a iya kwallon tennis a duniya.

Dukkansu 'yan wasan biyu za su nufi gasar Australian Open da birnin Melbourne zai karbi bakunci a ranar 16 ga watan Janairun 2017.