Kungiyar Chelsea ta maido da Ake Stamford Bridge

Gasar Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ake ya ci kwallaye uku a wasanni 12 da ya buga wa Bournemouth

Kungiyar Chelsea ta dawo da Natahan Ake Stamford Bridge daga Bournemouth inda yake buga wasanni aro.

Ake dan kwallon tawagar Netherland, ya koma Bournemouth da taka-leda aro a watan Yuni, inda ya ci wa kungiyar kwallaye uku a wasanni 12 da ya buga mata.

Dan kwallon mai shekara 21, bai buga wa Bournemouth wasan FA da aka doke ta a Millwall a ranar Asabar ba, domin ya kintsa kayansa zuwa Chelsea.

Chelsea tana mataki na daya a kan teburin Premier, kuma ita ce wadda aka zura wa karancin kwallaye a raga a gasar bana, inda guda 15 suka shiga ragarta bayan buga wasanni 20.

Kungiyar ta Chelsea tana da matasan 'yan kwallo 37 da suke buga wasanni aro a kungiyoyi da dama.