Mutane 4 sun mutu a hari da babbar mota a Jerusalem

Israeli security

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ana iya ganin alamun harbi da bindiga a gilashin motar

Wani Bafalasdine ya kashe 'yan kasar Isra'ila hudu a Jerusalem lokacin da ya danna da babbar mota cikin wani gungun sojojin, a wani abu da 'yan sanda suka ce hari ne na ta'addanci.

Wadanda suka mutun sun hada da mata uku da namiji guda, sannan wasu goma sha uku kuma sun jikkata.

'Yan sanda sun ce sojojin dake kusa sun harbe direban har lahira.

A watanni goma sha biyar da suka gabata, mutane daga Falasdinu sun sha kai hare hare da wuka da bindiga da kuma motoci akan 'yan Isra'ila.

Babban jami'in 'yan sandan Isra'ila, Roni Alsheich ya ce maharin na ranar Lahadin nan, Bafalasdine ne daga Gabashin Jerusalem.

Bidiyon da kyamarorin gefen hanya suka nada, ya nuna babbar motar lokacin da take tafiya a guje inda ta danna cikin sojojin, sannan kuma direban ya koma da baya inda ya sake bi ta kan mutanen da ya taka.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An tsaurara matakan tsaro a yankin da lamarin ya auku

Kafin harin na ranar Lahadi, Isra'ilawa talatin da biyar aka kashe a hare-haren da ake zargin Falasdinawa ko Larabawan Isra'ila da kai wa tun daga watan Oktoban 2015.

Isra'ila ta ce Falasdinawa fiye da dari biyu ne, akasarinsu maharan, aka kashe a lokacin.